﷽
بسم الله الرحمن الرحیم
ﯜ
ﯝ
ﯞ
ﯟ
ﯠ
ﯡ
ﯢ
ﯣ
ﯤ
ﯥ
ﯦ
ﯧ
هل اتى على الانسان حين من الدهر لم يكن شييا مذكورا ۱
gumi | Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata. |
---|
ﯨ
ﯩ
ﯪ
ﯫ
ﯬ
ﯭ
ﯮ
ﯯ
ﯰ
ﯱ
ﯲ
انا خلقنا الانسان من نطفة امشاج نبتليه فجعلناه سميعا بصيرا ۲
gumi | Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani, |
---|
ﯳ
ﯴ
ﯵ
ﯶ
ﯷ
ﯸ
ﯹ
ﯺ
انا هديناه السبيل اما شاكرا واما كفورا ۳
gumi | Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci. |
---|
ﯻ
ﯼ
ﯽ
ﯾ
ﯿ
ﰀ
ﰁ
انا اعتدنا للكافرين سلاسل واغلالا وسعيرا ۴
gumi | Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr. |
---|
ﰂ
ﰃ
ﰄ
ﰅ
ﰆ
ﰇ
ﰈ
ﰉ
ﰊ
ان الابرار يشربون من كاس كان مزاجها كافورا ۵
gumi | Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne. |
---|
ﭑ
ﭒ
ﭓ
ﭔ
ﭕ
ﭖ
ﭗ
ﭘ
عينا يشرب بها عباد الله يفجرونها تفجيرا ۶
gumi | Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa. |
---|
ﭙ
ﭚ
ﭛ
ﭜ
ﭝ
ﭞ
ﭟ
ﭠ
يوفون بالنذر ويخافون يوما كان شره مستطيرا ۷
gumi | Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne. |
---|
ﭡ
ﭢ
ﭣ
ﭤ
ﭥ
ﭦ
ﭧ
ﭨ
ويطعمون الطعام على حبه مسكينا ويتيما واسيرا ۸
gumi | Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme. |
---|
ﭩ
ﭪ
ﭫ
ﭬ
ﭭ
ﭮ
ﭯ
ﭰ
ﭱ
ﭲ
ﭳ
انما نطعمكم لوجه الله لا نريد منكم جزاء ولا شكورا ۹
gumi | (Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya. |
---|
ﭴ
ﭵ
ﭶ
ﭷ
ﭸ
ﭹ
ﭺ
ﭻ
انا نخاف من ربنا يوما عبوسا قمطريرا ۱۰
gumi | "Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa." |
---|
ﭼ
ﭽ
ﭾ
ﭿ
ﮀ
ﮁ
ﮂ
ﮃ
ﮄ
فوقاهم الله شر ذالك اليوم ولقاهم نضرة وسرورا ۱۱
gumi | Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki, |
---|
ﮅ
ﮆ
ﮇ
ﮈ
ﮉ
ﮊ
وجزاهم بما صبروا جنة وحريرا ۱۲
gumi | Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini. |
---|
ﮋ
ﮌ
ﮍ
ﮎ
ﮏ
ﮐ
ﮑ
ﮒ
ﮓ
ﮔ
ﮕ
ﮖ
متكيين فيها على الارايك ۖ لا يرون فيها شمسا ولا زمهريرا ۱۳
gumi | Sunã mãsu zaman ginciri, a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura. |
---|
ﮗ
ﮘ
ﮙ
ﮚ
ﮛ
ﮜ
ﮝ
ودانية عليهم ظلالها وذللت قطوفها تذليلا ۱۴
gumi | Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa. |
---|
ﮞ
ﮟ
ﮠ
ﮡ
ﮢ
ﮣ
ﮤ
ﮥ
ﮦ
ويطاف عليهم بانية من فضة واكواب كانت قواريرا ۱۵
gumi | Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau. |
---|
ﮧ
ﮨ
ﮩ
ﮪ
ﮫ
ﮬ
قوارير من فضة قدروها تقديرا ۱۶
gumi | ¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta. |
---|
ﮭ
ﮮ
ﮯ
ﮰ
ﮱ
ﯓ
ﯔ
ويسقون فيها كاسا كان مزاجها زنجبيلا ۱۷
gumi | Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne. |
---|
ﯕ
ﯖ
ﯗ
ﯘ
ﯙ
عينا فيها تسمى سلسبيلا ۱۸
gumi | Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil. |
---|
ﯚ
ﯛ
ﯜ
ﯝ
ﯞ
ﯟ
ﯠ
ﯡ
ﯢ
ﯣ
ﯤ
۞ ويطوف عليهم ولدان مخلدون اذا رايتهم حسبتهم لولوا منثورا ۱۹
gumi | Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa. |
---|
ﯥ
ﯦ
ﯧ
ﯨ
ﯩ
ﯪ
ﯫ
ﯬ
واذا رايت ثم رايت نعيما وملكا كبيرا ۲۰
gumi | Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba. |
---|
ﯭ
ﯮ
ﯯ
ﯰ
ﯱ
ﯲ
ﯳ
ﯴ
ﯵ
ﯶ
ﯷ
ﯸ
ﯹ
ﯺ
ﯻ
عاليهم ثياب سندس خضر واستبرق ۖ وحلوا اساور من فضة وسقاهم ربهم شرابا طهورا ۲۱
gumi | Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki). |
---|
ﯼ
ﯽ
ﯾ
ﯿ
ﰀ
ﰁ
ﰂ
ﰃ
ﰄ
ان هاذا كان لكم جزاء وكان سعيكم مشكورا ۲۲
gumi | (A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa." |
---|
ﰅ
ﰆ
ﰇ
ﰈ
ﰉ
ﰊ
ﰋ
انا نحن نزلنا عليك القران تنزيلا ۲۳
gumi | Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa. |
---|
ﰌ
ﰍ
ﰎ
ﰏ
ﰐ
ﰑ
ﰒ
ﰓ
ﰔ
ﰕ
فاصبر لحكم ربك ولا تطع منهم اثما او كفورا ۲۴
gumi | Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci. |
---|
ﰖ
ﰗ
ﰘ
ﰙ
ﰚ
ﰛ
واذكر اسم ربك بكرة واصيلا ۲۵
gumi | Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice. |
---|
ﭑ
ﭒ
ﭓ
ﭔ
ﭕ
ﭖ
ﭗ
ﭘ
ومن الليل فاسجد له وسبحه ليلا طويلا ۲۶
gumi | Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo. |
---|
ﭙ
ﭚ
ﭛ
ﭜ
ﭝ
ﭞ
ﭟ
ﭠ
ﭡ
ان هاولاء يحبون العاجلة ويذرون وراءهم يوما ثقيلا ۲۷
gumi | Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi. |
---|
ﭢ
ﭣ
ﭤ
ﭥ
ﭦ
ﭧ
ﭨ
ﭩ
ﭪ
ﭫ
ﭬ
نحن خلقناهم وشددنا اسرهم ۖ واذا شينا بدلنا امثالهم تبديلا ۲۸
gumi | Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa. |
---|
ﭭ
ﭮ
ﭯ
ﭰ
ﭱ
ﭲ
ﭳ
ﭴ
ﭵ
ﭶ
ﭷ
ان هاذه تذكرة ۖ فمن شاء اتخذ الى ربه سبيلا ۲۹
gumi | Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa. |
---|
ﭸ
ﭹ
ﭺ
ﭻ
ﭼ
ﭽ
ﭾ
ﭿ
ﮀ
ﮁ
ﮂ
ﮃ
ﮄ
وما تشاءون الا ان يشاء الله ۚ ان الله كان عليما حكيما ۳۰
gumi | Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima. |
---|
ﮅ
ﮆ
ﮇ
ﮈ
ﮉ
ﮊ
ﮋ
ﮌ
ﮍ
ﮎ
ﮏ
ﮐ
يدخل من يشاء في رحمته ۚ والظالمين اعد لهم عذابا اليما ۳۱
gumi | Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi. |
---|

قرآن - سوره ۷۶ انسان - آیه ۱